Gwamnatin ta tsara biyan tallafin man fetur din ne na watanni shida kacal a shekarar 2022.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta ci gaba da biyar kuɗin tallafin man fetur a zuwa watanni shidan farko na shekarar 2022.

Ministar kasafi da tsare-tsare Zainab Shamsuna Ahmed ce ta bayyana haka a yayin wani taro da aka yi a Abuja.

Ta ce gwamnatin ƙasar ta kammala shirin ci gaba da biyan tallafin man fetur har zuwa watanni shidan farkon shekarar 2022.

Sai dai gwamnatin ta ce za ta duba yuwuwar biyan tallafin man fetur ɗin bayan watanni shidan a nan gaba.

Tun tuni dai wasu daga cikin gwamnonin Najeriya ke roƙon gwamnatin ƙasar da ta cire tallafin ma fetur din baki ɗaya.

A baya an sha raɗe-raɗin cire tallafin wanda gwamnatin ta ce akwai batun hakan amma ba za ta yi gaggawar ɗaukar matakin hakan ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: