Sufeton ƴan sandan Najeriya Alƙali Usman Baba ya aike da dakarunsa manya-manya jihar Anambra.

An aike da muƙadashin sufeton ƴan sanda biyu, da mataimakan sufeton ƴan sanda biyar sai kwamishinonin yan sanda 14.
Haka kuma an aike da muƙadashin kwamishinonin ƴan sanda 31 da mataimakan kwamishinonin ƴan sanda 48.

Sanarwar da kakakin yan sandan Najeriya ya fitar ya ce dukkanin su za su je ne karƙashin kulawar mukaddashin sufeton yan sanda sashen binciken manyan laifuka.

Dukkanin jami’an su je ne domin sa ido kan zaɓen da za a gudanar a jihar ranar 6 ga watan Nuwamba mai kamawa.