Sanata Cliffford Ordia ya ce babu wani aiki da ma’aikatar damar da ruwan sha ta yi da kuɗaɗen da su ka ciyo a baya a don haka su ke so ministan reuwa Sulaiman Adamu ya zo domin yi bayani a kan badaƙalar kuɗaɗen.

Majalisar dattawan Najeriya ta yi watsi da bukatar ciyo bashi da ma’aikatar samar da ruwan sha ta buƙata har naira biliyan 287 da ɗoriya.
Ma’aikatar ta aike da buƙatar hakan ne domin gudanar da ayyukan samar da ruwan sha a birnin da karkara na ƙasar.

Majalisar ta buƙaci shugaban hukumar ya yi mata bayani dangane da bashin da aka ciyo a baya wanda aka yi da nufin samar da shirin samar da ruwan sha.

Shugaban kwamitin samar da ruwna sha a majalisar dattawa Sanata Cliffford Ordia ya buƙaci ministan ruwa ya bayyana a gaban majalisar domin yin bayan i a kan kuɗaɗen da hukumar ta ciyo bashi a baya da nufin ayyukan samar da ruwa a Najerya.
A baya hukumar samar da ruwan ta ciyo bashin dala miliyan 450, da kuma bashin dala miliyan 700 duka domin ayyukan samar d aruwa.
Shugaban kwamitin ya ce duk da amince masa na ciyo bashin a baya babu wani sakamako da ya bayyana a fili na ayyukan kudin da aka ciyo bashin.
A farkon shekarar da mu ke ciki ne Mujalar Matashiya ta zaƙulo wasu yankuna a jihar Kano da ke maƙaftaka da mahaifar ministan waɗanda ke shafe kwana da kwanaki kafin su sami ruwan da su ke sha bayan yin doguwar tafiya mai nisa.