Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya reshen jihar Zamfara ta ce matasa 172 ne su ka haukace a sanadin shaye-shayen kayan maye.

Hukumar ta ce hakan na daga cikin rahotannin da ta tattara cikin shekaru shida cikin matasan da su ka haukace a sanadin ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Mataimakin kwamandan hukumar Ladan Hashin ne ya bayyana haka a yau Alhamis a yayin taron da aka yi don yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin ɗalibai.

Ya ce daga watan Janairu zuwa watan Satumban da mu ke ciki an kama masu ta’ammali da miyagun ƙwayoyin 221 kuma guda 10 daga cikin su mata ne.

Ya ƙara da cewa mafi yawa daga cikin matasan da su ka kama su na gidan yari yayin da wasu ke cibiyoyin sauya ɗabi’a.

Jawabin ya ci gaba da cewa hanya mafi sauki na yaƙi da ɗabi’ar ita ce bin dokokin shan magani ƙarƙashin umarnin likitoci.

Taron da aka shirya don inganta ɗbi’un matasa ɗalibai don gujewa ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: