Rundunar yan sanda a Zamfara ta ce ƴan bindiga sun kashe jami’an staro uku a yayin wata musayar wuta a tsakaninsu.

Kakakin ƴan sandan jihar SP Muhammad Shehu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar.

Ya ce an kashe jami’an ne ranar Laraba a hanyar Ƙauran Namoda zuwa Shinkafi yayin d jami’an ƴan sanda hadin gwiwa da hukumar kare fararen hula su ke sintiri a titin.

A yayin artabun an kashe jami’in ɗan sanda guda ɗaya yayin da aka kashe jami’an hukumar kare fararen hula guda biyu.

Rundunar ta musanta labarin da ake yaɗa wa cewar ƴan bindiga sun hallaka jami’an tsaro 20 tare da ƙone gawar su.

Kakakin ya ce an ƙirƙiri labarin ne domin ska atsoro a zukatan al’umma kuma babu gaskiya a ciki.

Ya ce daga cikin ƴan bindigan akwai da dama da su ka tsere da raunin habin bindiga a jikin su.

Hukumar NSCDC ta ce ƴan bindigan da su ka kai harin sun kai su 150 kuma daga cikin jami’an da aka kashe akwai direban mota a ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: