Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya bayan halartar taron zuba hannun jari a saudiyya.

Shugaban ya halarci taron kashi na biyar wanda aka yi don zuba hannun jari daga ƙasashen duniya da sauran attajiran duniya.

Bayan kammala taron wanda aka ɗauki kwanaki a na yi, shugaban ya gabatar da ibadar umara shi da sauran muƙarraban sa.

Muhammadu Buhari ya yi wa ƙasar Najeriya addu’a a yayin da yake gabatar da umara.

Shugaba Buhari ya samu rakiyar manyan muƙarrabai a gwamnatin sa da kuma  shugabannin tsaro da masana a fannin tattalin arziki da zuba hannun jari.

Wasu dga cikin manyan attajirai a Najeriya sun halarci taron kamar Alhaji Aliko Ɗangode, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabi’u da Alhaji Ɗahiru Mangal.

Shugaba Buhari ya dawo Najeriya a ranar Juma’a bayan ya ziyarci Riyad babban birnin ƙasar saudiyya a ranar  Litiniin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: