Aƙalla yara 13 ne su ka rabauta da aikin tsagewar baki a asibin Malam Aminu Kano da ke Kano.

Asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano ya fara aiki ga yara da ake haifarsu da larurar tsagewar baki a sassa daban-daban.
Aikin da ake yii kyauta an fara ne bayan shugaban asibitin Farfesa Abdurrahman Abba Sheshe ya tura ma’aikatan sa don samun gogewa a ɓangaren.


Rakiya Adamu guda cikin ma’aikatan da ke ɓangaren masu larurar ta yi jawabi a kan yadda aka fara aikin da kuma matakin da ake a yanzu.
Ta ce sun lalubo mutanen da su ke da jarirai masu larurar da kuma tantance wa kafin tabbatar da cewar an yi musu aikin.
Dakta Bawa Tsafe Anas guda cikin likitocin da su ka yi aikin ya ce sun samu horo na musamman kafin fara gabatar da aikin kuma an yi wa mutanen aikin ne kyauta.
Ya ƙara da cewa wannan dama ce ga dukkanin jama’a don ganin sun amfana da aikin maimakon wasu da su ke amfani da su wajen bara ko kuma su dinga ɓoye su wasu ma su kashe su saboda yanayin halittar da ake haifarsu da shi.
Wasu daga cikin iyayen yaran da aka yiw a aikin sun yi wa Matashiya TV ƙarin haske a dangane da lamarin.
Wannan ne rukuni na biyu da aka sallama a yau bayan mutane bakwai na farko da tuni aka sallame su.
Dakta Bawa Tsafe ya yi kira ga iyaye musamman waɗanda ke da yara da aka haifa da wannan larurar don ganin sun ci moriyar aikin da ake yi kyauta.