Aƙalla mutane 19 ne su ka rasa rayuwarsu yayin da mutane 50 su ka jikkata a wani hari da aka kai asibitin sojoji na birnin Kabul da ke ƙasar Afganistan.

Maharan sun kai harin ne a yau Talata sannan su ka hallaka mutanen tare da raunata wasu daga ciki.
Nakiya biyu ce ta fashe sannan maharan su ka bi mutane da harbin bindiga.

Tuni aka kai mutanen da su ka sami rauni manhyan asibitoci da ke binin Kabul.

Mai magana da yawun gwamnatin Taliban ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce bama-bamai biyu ne su ka fashe kuma sun hanzarta zuwa wajen don duba halin da ake ciki.
Wannan ne karo na farko da aka kai mummunan hari da ya yi sanadiyyar rasa rayuwar mutane da dama tun bayan da yan Taliban su ka karɓi mulki a ƙasar.
Har zuwa lokacin da mu ke kawo muku wannan labari babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin.