Ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi a Najeriya NULGE ta karrama gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da lambar yabo mafi girma a matsayin gwamna mafi ƙwazo wajen tafiyar da harkokin ƙananan hukumomi a gwamnatin sa.

A yayin taron wanda ya gudana a ranar Laraba kuma mataimakin gwamnan  Kano Dr. Nasiru Yusif Gawuna ya wakilci gwamna.

Shugaban ƙungiyar Kwamared Ambali Akeem Olatunji  ya ce sun samar da kwamiti ne kafin tantance gwamna  da ya fi ƙwazo tare da zaƙulo guda cikin gwamnonin Najeriya.

Bayan fitar da gwamnoni uku ne kuma su ka gano gwana Ganduje shi ya fi sauran gwamnoni tafiyar da al’amuran ƙananan hukumomi cikin tsari.

Ya ce sun zaɓi gwamnan ne bisa nuna kulawa da aiki tuƙuru domin amfana wa mutanen kanan  hukumomi a cikin mulkin sa.

Taron masu ruwa da tsaki a ƙungiyar sun karrama kwamishinan ƙanann hukumomi a jihar Hon. Murtala Sule Garo a matsayin kwamishinan da ke koyi da tsarin mulkin gwamna ganduje don ci gaban ma’aikatan ƙananan hukumomi.

An zaɓi gwamna Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi kwazo kasancewar sa tsohon tsohon sakataren ƙaramar hukuma, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukuma sannan wanda ya zaƙulo da yawa daga cikin tsofaffin shugabannin ƙanan hukumomi tare da zuba su a cikin harkokin mulkin sa don samun nasarar tafiyar da tsarin gwamnatin yadda ayyuka za su dinga taba mutane na ƙasa.

Hon. Murtala sule Garo ya yi ƙarin haske a dangane da lambar yabo da akka bai wa gwmnan Kano Ganduje.

Wannan ne karo na biyu da ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi su ka karrama gwamnan da ya fi ƙazo a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: