Rundunar ƴan sandan a jihar Filato ta ce za ta ci gaba da garƙam majalisar jihar har sai an samar da daidaito a kan shugabancin.

Mataimakin sufeton ƴan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta 4 Mustapha Ɗandaura ne ya bayyana hakan a yayin zaman sulhu da aka yi da yan majalisun yau a ɗakiin taron na ƴan sanda da ke Jos.
Ƴan majalisu 24 ne su ka halarci zaman sulhun sai kuma tsohon shugaban majalisar da sabon shugaban wanda su ka zaɓa.

Shugabannin biyu kowa na ikirarin shi ne shugaban majalisar yayin da tsohon shugaban majalisar ya ce an janye jami’an tsaron d ake kula da shi.

Sufeton ƴan sandan ya nuna damuwa a bisa abin da ya faru a baya na zanga-zangar da ta faru a majalisar ya ce hakan barazana ce ga zaman lafiya a jihar.
Ƴan sandan sun bai wa ƴan majalisun dama domin sulhunta kansu tare da bayar da rahoto a kan zaan sulhun da za su yi.
Idan ba a manta ba ƴan majalisar jihar Filato sun tsige Abok Ayuba tare da maye gurbin sa da Sanda Yakubu.