BBCBBC

Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na jihar Anambra Don Adinuba ya ce rohoton da ke yawo na cewa mutane na tururuwan barin jihar yayin da ake zaben gwamna karya ne.

Adinuba ya bayyana cewa maimakon haka mutane na shigowa cikin jihar ƙwansu da ƙwarkwatarsu musamman wadanda suka cancanci yin zaben gwamnan wanda ake gudanar dashi a yau Asabar 6 ga watan Nuwamba.

Ya magantu a kan lamarin ne a cikin wata sanarwa wadda aka rabawa manema labarai

Ya karyata rahotan inda ya ce mutanen Anambra basu nuna tsoron yiwuwar barkewar ko wani rikiciba kafin  lokacin da bayan zaben.

Ya ce “Mutananmu sun nuna tushensu don haka yawanci suna yin rajistar katin zabe ne a jihar ko da kuwa basa cikin garin ne”.

Ya bayyana cewa mutane da dama da ke aiki a birane a Anambra su kan yi rijistarsu a mahaifarsu sannan da hutun aiki da aka bayar a ranar Alhamis da Juma’a da dama sun tafi mahaifarsu don kaɗa kuri’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: