An ceto magen da ranta kuma ta na cikin ƙoshin lafiya.

Hukumar kashe gobara a Kano ta ceto wata mage da ta faɗa rijiya.

Mai magana da yawun hukumar Saminu Yusuf be ya bayyana hakan a yau a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Magen ta faɗa wata rijiya ne a unguwar Kawon Mai Gari kusada makarantar Islamiyya ta Usmaniyya.

Bayan samun kiran a ranar Lahadi dakaruj hukumar su ka hanzarta zuwatare da ceto magen.

Hukumar ta shawarci masu rijiyar su rufe ta don kare afkuwar hakan a nan gaba.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: