Babban bankin Najeriya CBN ya ce an samu raguwar samun jabun kudi a shekarar 2020 a rahoton da ya tattara.
Bankin ya bayyana haka ne bayan tattara sakamako da ya samu daga jami’an staro, bankuna da wasu hukumomi masu alaƙa da hakan.
A wata sanarwa da su ka fitar, bankin ya ce a shekarar 2020 sun samu jabun kuɗi na naira dubu da na naira 500 na ƙimar kudi naira miliyan 64.71, sabanin shekarar 2019 da aka sami naira miliyan 84,934.
Wannan ƙididdigar da su ka yi ce ta tabbatar da cewar an samu ƙarancin jabun kudin a shekarar da ta gabata.
Wannan an nuni da cewar samun jabun kudin ya ragu da kashi 20.80 cikin ɗari.
Bankin ya buƙaci bankuna da su mayar da hankali wajen yaƙi da jabun kudin tare da haɗa kai da jami’an tsaro don ganin an samu nasarar yaƙi da buga jabun kuɗin da kuma yawaitar su a cikin jama’a.