Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da kashe babban sojan sama mai ritaya AVM Muhammad Maisaka wanda yan bindiga suka kai masa hari a gidansa dake Rigasa ƙaramar hukumar Igabi ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda na jihar ASP Muhammada Jalige ya tabbatar da wa da kamfaninn dillancin labarai a Najeriya NAN aukuwar lamarin ranar Talata a kaduna.

Kakakin ya ce ƴan bindigan sun kashe shi ne bayansun je gidan sa.

Ya ce bayan samun labarin kwamishinan yan sandan jihar Mudassiru Abdullah ya umarci yan sandan yankin da su yi gaggawar zuwa wajen da abin ya auku.
A cewarsa “An kai gawar sa ma’adanar da ake ajie gawarwakin mutane da ke asibiti, inda kuma aka wuce da mai gadin gidansa asibiti domin kulawa da lafiyar sa”.
Ya kara da cewa za su bayar da cikakken bayani a kan faruwar lamarin a nan gaba
Ƴan sanda sun bukaci mazauna Kaduna da su yi gaggawar gabatar wa jami’an tsaro bayanai masu amfani da zasu bayar da damar kama wadanda suke da alhakin aika-aika.