Hukumar kula da masu yi wa ƙasa hidima a Najeriya NYSC ta gargaɗi masu yi wa ƙasa hidima don ganin sun duƙufa a kan abin da aka saka su.

Babban darakta a hukumar Shu’aibu Ibrahim ne ya sanar da haka ya na mai cewa babu hutun makonni biyu bayan zama a sansanin yi wa asa hidima.

Shugaban ya gargaɗi masu yi wa ƙasa hidima da su kasance sun ƙauracewa aikata dukkan abin da ya saɓa da ƙa’idar hukumar.

Haka kuma ya ja kunnen ɗaliban da su kaucewa zuwa wajen fati, fitar dare ko ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Shu’aibu Ibrahim ya hori ɗaliban da su mayar da hankali a kan darrusan da su ka koya don sun amfani rayuwarsu a yanzu da ma nan gaba.

Maƙasudin sanarwar ita ce jaddada hani ga hutun makonni biyu bayan zaman ɗaliban a sansanin su da sunan zuwa hutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: