Hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya kwastam ta ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakar Najeriya da Benin da sauran iyakokin Najriya.

Matakin hakan na zuwa ne bayan samun bayanai a kan wasu da ke fasa kwaurin shinkafa daga iyakokin Najeriya.

Hukumar ta ƙara yawan jami’an ta a iyakokin Najeriya musmman iyakar Najeriya da ƙasar Benin.

Bayanai sun tabbatar da cewar akwai tilin shinkafa da aka ajiye a ƙasar Benin wadda aka sarrafa daga ƙasar India da Thailand.

Shugaban ƙungiyar masu sarrafa shinkafa a Najeriya ne ya bayar da bayanin hakan ga hukumar hana fasa ƙwauri a Najeriya lamarin da ya sa hukumar ta ƙara tsaurara matakan tsaro a iyakokin.

A ranar Lahadi gwamnatin Najeriya ta ce an samu yawan shinkafar da ake fasa ƙwauri zuwa cikin ƙasar bayan da aka haramta shigo da ita stawon lokaci.

Hukumar kwastam ta ce ta haɗa kai da sauran jami’an tsaro don ganin an ci gaba da sa ido sosai domin tabbatar da bin doka da oda kamar yadda aka gindaya a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: