Daga Amina Tahir Muhammad Risqua

Majalisar  wakilai a Najeriya ta bukaci ministan babban birnin tarayya Abuja Mohammed Bello ya bayyana a gabanta kan rashin tsaro da lalacewar ababen more rayuwa.

Ɗan majalisa wakilai Toby Okechuku ne ya gabatar da ƙudirin a gaban majalisar ranar Talata.

Majalisar ta ce Abuja na fuskantar barazanar tsaro hakan ya sa su ka buƙaci ya bayyana a gabanta don yin bayani a kan halin da ake ciki.

Ɗan majalisar wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, ya ce, majalisar na sane da irin ikon da aka baiwa ministan babban birnin tarayya kamar yadda sashe na 302 na kundin tsarin mulkin kasa ya tanada.

Majalisar ta lura cewa Abuja ba ta taɓa tsintar kanta a kan rashin tsaro kamar yadda take a yanzu ba, saboda yawaitar ƴan fashi da masu laifuka.

Wannan na zuwa ne bayan da wasu ƴan bindiga su ka sace malaman jami’a da ƴaƴan su a jami’ar Abuja.

Leave a Reply

%d bloggers like this: