Rundunar yan sanda a Sokoto ta musanta labaran da ake cewar ƴan bindiga na iko da wasu ƙauyuka a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar Sanusi Abubakar ne ya bayyana haka a bayan gudanar da bincike su ka gano labarin ba gaskiya bane.

ɗan majalisa mai wakiltar Sabon Birni a jihar ne ya bayyana wa BBC cewar ƴan bnindiga na iko da ƙayuka sama da 20 a jihar.

Bayan samun labarin haka ne rundunar ta fara gudanar da bincike a kan batun sannan ta gano cewar babu wani ƙauye da yan bindiga ke iko da shi.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewar sun dukufa ka’in da na’in don ganin an magance matsalar tsaro a yankunan da abin ke faruwa a jihar.

Sannan su na amfani da ƙwarewa don ganin an samu nasara a kan magance ta’addancin ƴan bindiga da su ka saka a gaba.

An haɗa kai da ƴan sanda, rundunar sojin sama da rundunar sojin ƙasa da na ruwa don ganin an yaƙi ta’addanci da sauran muggan laifuka da su ka addabi jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: