Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna sun daƙile wani hari da ƴan bindiga su ka yi yunƙurin kai wa a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Dakarun cin ci ƙarfin jami’an tsaron ne lamarin da ya kai ga sun raunata da yawa daga cikin ƴan bindigan.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ne ya sanar da haka a sanarwar da ya sanya wa hannu ranar Laraba.

Rundunar ta samu bayani a kan yunƙurin tare babbar hanyar da yan bindigan su ka so yi a ranar 9 ga watan Nuwamban da mu ke ciki.

Bayan samun bayanai a kan haka ne dakarun su ka bazama tare da tarwatsa su lamarin da ya sa ƴan bindigan su ka gudu cikin daji ɗauke da raunin harbi a jikinsu.
Rundunar ta buƙaci al’umma da su kai rahoton duk wani da su ka gai ɗauke da raunin harbi a jikin sa don gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin gaggawa.
An ɗauki tsawon lokaci ba a samu labarin tare babbar hanyar mota daga Kaduna zuwa Abuja ba, bayan da matafiya su ka sauya salon tafiyar su zuwa jirgin ƙasa.