Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce aƙalla mutane 4,369 ne su ka gudu daga gidan yari a kasar daga shekarar 2020 zuwa yanzu.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka a buja a yayin taron da aka shirya ranar Alhamis.

Ya ce daga cikin mutanen da su ka gudu 984 kacal aka sake kama wa bayan bincike a aka yi.

Sai dai gwamnatin na da bayanai a kan dukkanin waɗanda su ka gudu tare da hoton yatsan kowa a cikin su.

Ya kara da cewa duk da sun gudu daga gidan yarin, hakan ba ya na nufin sun ɓuya ba za a iya sake kama su ba.

Ƴan bindiga na ɓalle gidajen yari a Najeriya musmaman kudanci tare da kuɓutar da wadanda ake tsare da su a ciki.

Hari mafi ɗaukar hankali shi ne na gidan yarin jihar Imo wanda aka kuɓutar da mutane dubunnai a ciki, sai dai gwamnatin ta ce wasu daga ciki sun koma ne da ƙafarsu.

Wannan wani salo ne da ƴan bindiga ke yi a kudancin ƙasar wanda ake zargin yan ƙungiyar IPOB da kai hare-hare gidan yarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: