Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wasu ma’aurata mata da miji a Malammadori ta jihar.

An kashe mutanen biyu a ranar 13 ga watan da muke ciki da msialin ƙarfe 2:30 na dare.

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar ya ce wasu da ake zargin ƴan bindiga ne su ka je gidan ma’auratan da daddare sannan su ka kashe mata da miji.

Sun je gidan mutanen da ke ƙauyen Kebberi sannan su ka harbe su da bindiga.

An kashe Ahaji Musa da matasa Hajiya Adama wanda ake zargin wasu aka ɗauka da nufin kashe su har lahira.

Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa ƴan bindigan ba su ɗauki komai a cikin gidan ba bayan sun kashe su.

Sai dai an sami wasu wayoyin hannu guda biyu da ake zargin na ƴan bindigan ne kuma za su gudanar da bincike a kan su.

Sannan an cafke was mutane biyar da ake zargi da hannu a kan mutuwar ma’auratan biyu wanda a halin yanzu ake kan bicike a kan su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: