Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta yi barazanar shiga yajin aiki nan da makonni uku a nan gaba.

Ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wa’adin makonni uku don cika alƙawuran da ta ɗaukar musu ko kuma su tsunduma yajin aikin.
Hakan ya biyo bayan wani zaman majalisar ƙoli da ƙungiyar ta yi a Abuja.

Ƙungiyar ta ce ta yanke wannan hukunci ne duba ga rashin cika alƙawuran da gwamnatin ƙasar ta gaza cikawa tare da biyan su haƙƙoƙin su.

Shugaban da ya jagoranci zaman Farfesa Emmanuel Osodoke ya ce wannan ce mafita guda ɗaya da su ka cimma kuma ita ce hanyar da za su ɗauka.
Ƙungiyoyi da dama sun sha ɗaukar irin wannan mataki tare da nuna gazawar gwamnatin wajen rashin cika alƙawuran da ta ke ɗauka wanda hakan ke sa su tsunduma yajin aikin.