Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta na yin duk mai yuwuwa don ganin ta fito da hanyoyin da za su karyar da farashin kayan abinci a ƙasar.

Minsitan gona a ƙasar Dakta Mohammed Abubakar ne ya bayyana haka ranar Litinin yayin taron da aka yi a Abuja.
Ya ce gwamnatin ƙasar na sane da halin da talakawa ke ciki da kuma irin tsadar farashin kayan abinci kuma su na bin hanyoyin da za su kawo sauki a lamarin.

Ya kara da cewa ƙoƙarin da su ke yi shi ne ganin ƴan ƙasar na samun abin da za su ci a rana ba tare da sun sha wahala ba.

Taron da aka yi don gudanar da bincike a kan al’amuran da su ka shafi noma zai samar da hanyar da za ta sauƙaƙa wa jama’ar ƙasar na ganin an samu sauƙin farashin kayan abinci.
Haka kuma gwamnatin za ta tabbatar ta bayar da tallafi ga manoma kai tsaye ba tare da wasu da ke shiga rigar manoman ba tare da cin gajiyar tallafin gwamnatin.