Hukumar kula da jiragen kasa a Najeriya sun fara yajin aiki har na tsawon kwanaki uku a yau Alhamis.
Ma’aikatan hukumar sun bayyana cewa ya kamata Gwamnati tai musu karin albashi da kuma tabbatar da walwala a cikin aikin su .
A ranar asabar din da ta gaba ta ne dai ministan sufurin jiragen kasa Rotimi Amaechi ya yi wata ganawa da shugaban kwadago domin cimma matsaya a kan tafiya yajin aiki da su ka shirya yi amma hakan na sa ya gaza cimma ruwa.
Hukumar ta bayyana cewa ta shirya zama da kungiyoyin ma aikata domin samun daidaito a tsakanin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: