Majalisar dinkin duniya ta yi Allah wadai da kisan wasu mutane a kasar Sudan.
Majalisar ta zargi sojojin kasar da yin amfani da harsashi mai kisa wajen kashe masu zanga-zanga.
Mutane 15 ne su ka mutu a yayin da ake gudanar da zanga-zanga a kasar Sudan ranar Laraba.
Sanarwar da majalisar ta fitar ra ce abin kunya ne kisan masu zanga-zangar da aka yi kuma ta na Allah wadai da kisan mutanen.
Janar Abdel Fatah ne a jagoranci juyin mulki a kasar Sudan a ranar 25 ga watan Oktoban da ya gabata.
Kuma an kifar da mulkin farar hula na rikon kwarya daga hannun Abdalla Hamdok, lamarin da ya haifar da hargitsi a kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: