Akalla mutane 121 ne su ka kamu da cutar amai da gudawa yayin da aka samu wasu uku su ka mutu a sanadin cutar a jihar Nassarawa.
Kwamishinan lafiya na jihar Dakta Liman Mohammed ne ya sanar da haka a Lafiya babban birnin jihar.
Ya ce an samu rahoton mutane 89 sun kamu da cutar a karamar hukumar Awe ta jihar tare da samun mutuwar mutum guda.
Sai kuma wasu mutane da su ka kamu da cutar a karamar hukumar Obi tare da smaun rahoton mutuwar mutane biyu.
Jawabin da kwmaishinan ya yi ya ce wadanda su ka mutu yara ne yan kasa da shekaru goma.
Tuni gwamnatin ta samar da magunguna don ganin an aki cutar wadda ke barazana ga rayyuwar jama’a.
Haka kuma gwamnatin ta bukaci al’ummar jihar da su kasance masu kula da lafiyar su tare da horon ma’aikatan lafiya da su mayar da hankali a kan aikin su don ganin mutane sun samu kakkyawar kulawa daga gare su.


