Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta amince wa kamfanonin samar da wutar lantarki na NERC da su yi kari kudin wutar.
NERC ta bayyana cewa ta umarci kamfanonin wutar lantarkin da su kara kudin wutar sakamakon halin da kasuwanci ya shiga ciki.
Ta ce mutanen da su ke amfani da wutar lantarki za su ga sauye sauye a watan Disamba mai kamawa sakamakon tsarin da gwanmatin tarayya ta shigo da shi.
Ta bayyana cewa akwai yiwuwar masu amfani da wutar za a kara musu kudin wuta a kan yadda su ke biya a baya bisa tabbatar da karin da a ka bai wa kamfanoni su yi a watan Disamba mai kamawa.
Hukumar NERC mai kula da sha’anin wuta a Najeriya za ta bayyana sababbin tsare tsaren farashin kudin wutar.
Hukumar ta ce za ta yi zaman ta a watan Disamba domin tattaunawa don samun mafita a kan wasu abubuwa da su ka shafi harkar wutar lantarki da kuma rarraba wa ga al umma.
Haka zalika dokar kasa ta bada umarnin duk bayan wata shida ko shekaru biyar za a dunga duba farashin wuta don ganin ci gaban da a ka samu a harkar.


