Ƙungiyar ma’aikatan jiragen ƙasa a Najeriya sun sanar da janye yajin aikin da su ka fara na gargadi ga gwamnatin a kan rashin duba buƙatun su.

Ƙungiyar ta shiga yajin aikin na tsawon kwanaki uku don jan kunnen gwamnati na ganin ta dube su tare da cika musu buriun su.
Shugaban ƙungiyar Kwamared Luka Ajiji ya sanar da shiga yajin aikin a ranar Alhamis sanadin rashin martaba aikin su.

Ƙungiyar ta miƙa wa gwamati buƙatun su na samar da walwalar ma’aikata da kuma karin albashi da sauran buƙatu sai dai an gaza cimma matsaya.

Tun a baya ƙungiyar ta yi barazanar tsunduma yajin aikin matuƙan ba a duba bukatunsu ba.
Bayan shiga yajin aikij da su ka fara a ranar Alhamis, gwamnatin ta tsayar da wakilai wadanda su ka tattauna da ƴaƴan ƙungiyar lamarin da ya sa aka cimma matsaya.
Ƙungiyar ta janye yajin aikin nata a yau kwanaki uku da fara wa.