Majalisar dattijai a Najeriya ta miƙa kundin sabuwar dokar hukumar zaɓe ga shugaba Buhari domin amincewar sa a kai.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/12/mn-1.jpg)
Sabuwar dokar zaɓen da aka gyara wadda za ta bayar da damar shigar da sabbin dokoki musamman ta hanyar amfani da fasahar zamani.
Babban mataimaki ga shugaban Najriya a kan harkokin majalsiar dattijai Babajide Omowoare ne ya sanar da haka a ranar Juma’a.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2021/10/DSC_9894-scaled.jpg)
An miƙa wa shugaban dokar da aka yi wa gyare-gyare domin cika tsarin kundin mulkin ƙasa.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/02/matashiya-photo-2.jpg)
Tun a ranar Talata makalisar dattawan Najeriya ta karɓi rahoton gyaran dokar hukumar zaɓen wadda kwamitin ya kammala aikin sa a kai.
Shugaba Buhari na da damar duba dokar tare da saka hannu a kan ta daga ranar da aka gabatar masa da ita zuwa kwanaki talatin masu zuwa.
Hakan na ƙarƙashin saseh na 58 (3) na kundin dokar Najeriya wanda aka yi wa gyare-gyare a shekarar 1999.