Asusun bayar da lamuni na duniya ya buƙaci shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta janye tallafin man fetur da na wutar lantarki kafin shekarar 2022.

Hakan ya biyo bayan wani bincike da wakilan su ka gudanar a Najeriya bayan sun kawo ziyara ƙasar.

Sanarwar da asusun ya fitar ya ce sun fuskanci wgamnatin ƙsar ta fi bai wa ɓangaren wuta da na man fetur fifiko a harkokin gudanarwar kudi.

Bayar da muhimmanci  a ɓangaren harkokin gudanarwar kudi da gwamnatin ke yi a bangaren mai da wutar lantarki ke kawo rashin ci gaba a ƙasar.

Sai dai asusun ya shawarci gwamnatin da ta samar da wata hanya da za ta rage radaɗin janye tallafin a ɓangarorin guda biyu.

Gwamnatin ƙasar ta tsara bayar da tallafin man fetur na tsawon watanni shida a shekarar da ake daf da shiga, yayin da su ka bayar da sanarwar cire tallafin wutar lantarki a watan Disamba mai kama wa.

Mutane na ta’allaƙa a kan man fetur da wutar lantarki wanda wasu ke kallon hakan a matsayin wata gaɓa da talaka ke morar gwamnatin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: