Gwamnatin Taliban ta haramta wa mata fitowa a wasannin kwaikwayo a ƙasar Afghanistan.

Wannan na daga cikin sabbin dokokin da gwamnatin Taliban ta saka na ganin ta ci gaba da bayyanar da manufofin ta a ƙasar.

Sannan gwamnatin ta sanar da saka doka a kan mata ƴan jarida da wajibi ne su dinga rufe kan su.

Haka kuma an haramta nuna fim a talabiji wanda ya saɓa da shari’a da kuma al’adun ƙasar.

Daga cikin dokokin guda takwas an haramta wa maza nuna tsaraicin su a cikin wasan kwaikwayo.

Gwamnatin ta dakatar da nuna wani fim da ke cin mutuncin addini ko cin mutuncin ƴan ƙasar Afghanistan.

Haka kuma ba za ta lamunci haska duk wani fim da ke nuna al’adu ko tallata al’adun wasu ƙasashen ba.

Gwamnatin Taliban na ci gaba da saka dokoki tun bayan da ta karɓe mulki a ƙasar Afghanistan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: