Ƙungiyar likitoci masu lura da masu ciwon zuciya a Najeriya sun ce a na haifar jarirai 80,000 masu larurar ciwon zuciya a duk shekara.

Shugaban ƙungiyar Dakta Uvie Onakpoya ne ya bayyana haka a yayin taron ƴan jarida da aka yi a asibitin koyarwa na Usman Ɗan Fodiyo da ke Sokoto.
Hakan ya biyo bayan nasarar da su ka yi wajen yi wa jarirai biyu aiki bayan an tabbatar su na da larurar ciwon zuciya.

Ya ce daga cikin jarirai 80,000 da ake haifa masu larurar ciwon zuciya guda 200 ne kaɗai iyayensu ke samun dama don a yi musu aiki.

Sai dai zuwan annobar Korona ta tilastawa manyan asibitoci a Najeriya gudanar da aikin masu larurar ciwon zuciya ba tare da samun tallafi daga ƙasashen ketare ba.
Shugaban ya ce a halin yanzu akwai ƙwararrun likitoci da su ke gudanar da aiki ga masu ciwon zuciya ba tare da sun tsallaka ƙasashen ƙetare ba.
Sannan ya buƙaci gwamnati da ta dakatar da kai likitoci ƙasashen ƙetare domin samun horo a kan aikin ganin yadda ake da ƙwararru a Najeriya.