Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Mayaƙan Boko Haram Sun Hallaka Jami’an Tsaro 366 A Arewa Maso Gabashin Najeriya

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana kididdigar jami’an tsaron da su ka mutu a sanadiyyar hare-haren mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

Sojoji da ƴan sanda da sauran jami’an staron  hadin gwiwa 366 ne su ka mutu a hare-haren mayaan Boko Haram daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2021.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara a kan al’amuran staro a Najeriya Babaana Munguno ya ce sun karɓi  tsofaffin mabiya Boko Haram 15,000 waɗanda su ka tuba tare da miƙa kansu ga gwamnati.

Ya ce gwamnatin za ta ba su kulawa don ganin an sautya tunanin su na baya zuwa sabuwar rayuwa.

Daga cikin mabiyan da su ka tuba akwai mata da yara sai kuma maza da su ke ƙarƙashin Boko Haram a baya.

Mabiya Boko Haram na tururuwar kai kansu ga hukuma tun bayan mutuwar tsohon shugaban ƙungiyar Abubakar Sheƙau.

Sai dai har yanzu gwamnatin ba ta bayyana sunayen masu ɗaukar nauyin mayakan ba tun bayan da ta gano da yawa masu taimaka musu a kasar.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: