Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Ƙone Ofishin Ƴan Sanda A Imo

Rundunar ƴan sandan jihar Imo ta tabbatar da kashe jami’inta guda tare da ƙone ofishin jami’an a yau Talata.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne su ka kai harin a safiyar yau Talata kamar yadda ƴan sandna su ka bayyana.

An ƙone ofishin ƴan sanda da ke Arondizuogu a yankin karamar hukumar Ideota ta jihar.

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan wani rikici ya faru tsakanin wasu matasa da ake zargin yan ƙungiyar IPOB ne da jami’an sojisu ka yi a jihar.

A yayin arangamar da aka yi ranar Litinin an ƙone shaguna bakwai otel da wasu motoci a yankin Awomana ta jihar Imo.

Mai magana da rundunar sojin ƙasa yanki na 82 Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka ya ce dakarun Operation Golden Down ne su ka daƙile harin da aka kai musu.

Jihar Imo wadda cibiya ce ta ƙungiyar IPOB masu rajin balle wa daga Najeriya tare da kafa kasar BIAFRA.

Wasu daga cikin dattawan ƙabilar Ibo sun buƙaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya baki don sakin shugaban IPOB Nnamdi Kanu wanda a halin yanzu ke tsare a hannun jami’an DSS.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: