Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Awanni Kaɗan Da Tare Hanyar Kaduna Ƴan Bindiga Sun Sake Sace Wasu Mutane A Hanyar Abuja

Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne ɗauke da makamai sun sake tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a yammacin jiya Litinin.

Kwana guda da sace mutane tare da kashe wasu a babbar hanyar, ƴan bindigan sun sake tare babbar hanyar tare da sace wasu mutane da dama.

Wani da abin ya faru a gabansa ya shaida cewar ya hangi motar Zamfara mai ɗaukar mutane 18 da wasu motoci hudu duka babu kowa a ciki.

Al’amarin ya faru a yammacin ranar Litinin ƙasa da awanni 24 bayan ƴan bindigan sun tare babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadi.

Motocin da aka hanga yashe a kan titi akwai alamun harbin bindiga a jikin su, kuma wajen da abin ya faru tazarar kilo mita biyar ne da wrin da aka tare ranar Lahadi.

Shaidar da abin ya faru a gabansa ya ce jami’an tsaro sun je wajen amma kafin zuwna su ƴan bindigan sun tafi da mutanen da su ka sace cikin daji cikin kanaƙanin lokaci.

Yayin da mu ka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya ce zai bincika a kan lamarin kuma har lokacin da mu ke kawo muku labarin ba mu ji daga gareshi ba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: