Gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya kawo karshen annobar Korona nan da ƙarshen shekarar 2022.

Manajan tafiyar da al’amuran kwamitin a kan yaƙi da cutar Dakta Mukhtar Muhammad ne ya bayyana haka a yayin wani taro da aka yi a Abuja.
Ya ce gwamnatin ƙarsar na shirin kawo ƙarshen annobar cutar daga yanzu zuwa watan Disamba na shekarar 2022.

Taron da aka yi don tinkarar babban taro na ƙasa da za a yi a watan Disamban da mu ke ciki domin gano nasara da kuma hanyar kawo karshen annobar.

Tsarin kawo karshen cutar zai kalli ɓangaren ci gaban harkokin lafiya da kuma bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Ya ƙara da cewa kawo karshen annobar Korona kafin ƙarshen zangon mulkin da ake ciki na daga cikin manufofin gwamnatin shugaba Buhari.
Gwamnatocin duniya na kallon annobar Korona a matsayin abin da ya kawo koma baya a kan tattalin arziƙin ƙasa a fadin duniya baki ɗaya tare da kawo tsaikon al’amura tun bayan bullar cutar.