Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Rahoton Kwamitin Binciken Rikicin #ENDSARS Ƙarya Ne – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labarai da al’adu a Najeriya Alhaji Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton da aka fitar kan rikicin ENDSARS a jijar Legas.

Kwamitin bindike sun ce sojojin Najeriya sun kashe wasu mutane a yayin da su ke gudanar da zanga-zanga a jihar.

Ministan ya danganta rahoton da labaran ƙarya wanda ake yada wa a kafafen sadarwar zamani na Intanet.

Alhaji Lai Mohammed ya b ayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai da ya shirya a Abuja babban birnin Najeriya.

Ministan ya ce sun yi watsi da rahiton da aka fitar kan rikicin ENDSARS a Lekki da ya faru ranar 20 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

Ya ce gwamnatin Najeriya ba za ta taba barin hukumomin tsaro su ci zarafi ko take haƙƙin ƴan ƙasar ba.

Wannan ne dalilin da ya sa gwamnatin ta soke rundunar SARS tare da kafa kwamitin bincike a kai.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: