Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Za A Fara Biyan Ƴan Najeriya 5,000 Na Rage Raɗaɗin Janye Tallafin Man Fetur

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta fara biyan ƴan ƙasar naira dubu biyar a kowanne wata a matsayin wani kaso don rage raɗaɗi kafin cire tallafin man fetur.

Ministar kuɗi da tsare-tsare Zainab Shamuna Ahmed ce ta sanar da haka a yayin wani taro da aka yi yau Talata a Abuja.

Ta ce za a biya mutane miliyan 30 zuwa 40 naira dubu biyar a duk wata domin rage raɗadin cire tallafin mai da za a yi a shekarar 2022.

Ta ƙara da cewa za a tantance adadin mutanen da za su karɓi kuɗin bayan janye tallafin man tare da duba lalitar gwamnatin don duba abin da zai yuwu a kai.

Tun a baya ministar ta ce an tsara bayar da tallafin man fetur ne kaɗai na tsawon watanni shidan farkon shekarar 2022.

Daga bisani kuwa asusun bayar da lamuni a duniya ya buƙaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gaggauta janye tallafin man fetur da na wutar lantarki baki ɗaya domin samar da ci gaba a ƙasar.

Mutane da dama na kallon man fetur da wutar lantarki a matsayin wata kafa da talakan ƙasa ke kurɓar romon demokaradiyyar Najeriya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: