Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Ƴan Sudan Sun Yi Zanga-Zanga Ƙin Goyon Bayan Yarjejeniya Da Sojoji

Mutane a ƙasar Sudan sun gudanar da zanga-zanga a bisa yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin hamɓararren firaministan kasar da sojoji.

Dubban mutane sun mamaye babban binrin ƙasar da sauran birane a don nuna rashin goyon baya a kan yarjejeniyar da su ka yi.

A wasu yankunan ƙasar ƴan sanda sun harba hayaƙi mai saka hawaye a kan masu zanga-zangar.

Manyan ƴan siyasa da ƙungiyoyi a ƙasar sun yi watsi da yarjejeniyar da aka ƙulla a tsakanin Abdalla Hamdok da sojoji.

Sojoji sun hamɓarar da gwamnatin farar hula a ƙasar tare da jan ragamar shugabancin kasar, sai dai daga bisani sun mayarwa da shugaban na mulkin farar hula kujerar sa.

Hakan ya zo ne bayan yarjejeniya da sojojin su ka yi da hamɓararren firaministan wanda wasu daga ƴan ƙasar ke kallon hakan a matsayin butulcewa goyon bayansu.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: