Ƙungiyar dillalan man fetur a Najeriya ta goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur da ake shirin yi a shekarar 2022.

Shugaban ƙungiyar ta ƙasa Chinedu Okoronkwo ne ya sanar da haka ranar Juma’a.
Ya ce ƙungiyar na goyon bayan tsarin duba ga sabuwar dokar man fetur wadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya wa hannu.

Ya ce cire tallafin zai bayar da dama ga yan kasuwa don buƙasa kasuwancin su domin bunƙasa ɓangaren.

Gwamnatin Najeriya ta ayyana shirinta na cire tallafin man fetur ɗin a shekarar 2022.
Sannan ta gabatar da ƙudirin bayar da tallafi ga yan ƙasar mutane miliyan 30 zuwa 40 za a ba kowannen su naira dubu biyar don rage raɗaɗin tallafin.
A ɓangaren majalisar dattawan ƙasar kuwa ta ce babu wnai ɓangare a kasafin 2022 da zai bayar da damar raba wa mutane kudin.
Shugaban kwamitin lura da kasafi a majlisar ne ya bayyana haka a makon da mu ke gab da bankwana da shi tare da cewar kudin tallafin da aka shirya bai wa mutane ya zarce tallafin man da gwamnatin ke bayarwa.