Hukumar lafiya ta duniya WHO ta sanar da ɓullar sabuwar annobar Korona nau’in Omicron wadda ta bayyana a ƙasar Afrika ta Kudu.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar yau Asabar wadda ta ce sun smai rahoton ɓullar sabon nau’in cutar a ranar 24 ga watan Nuwamban da mu ke ciki.
An samu wasu ɗauke da cutar wadda hatsarinta ya zarce dukkan nau’in cutar Korona da aka sani a baya.

An fara samun masu ɗauke da nau’in cutar tun a ranar 9 ga watan Nuwamban da mu ke ciki.

Tuni aka aike da dakarun da ke bibiya tare da bayar da shawarwari domin ci gaba da bibiya a kan nau’in cutar don fitar da cikakken bayani a kan ta.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da bibiya tare da tattara bayanai a kai sannan za ta bayyana wa jama’a halin da ake ciki idan akwai buƙatar hakan a nan gaba.
Sannan ta shawarci al’umma da su ci gaba da bin dokokin kariya daga kamuwa daga cutar domin rage yaduwarta a cikin jama’a.