Hukumomin tsaro a Najeriya sun tabbatar da yuwuwar kai hare-hare a wasu iyakokin ƙasar.

Bayan fitar da bayanin don shirin ko ta kwana an aike da jami’an tsaro iyakokin da ake zargin ƴan bindiga na iya kai hare-hare a Najeriya.

Jihohin da abin ya shafa sun ƙunshi Legas, Oyo, da kuma jihar Ogun.

Hukumar tsaro ta DSS da hukumar hana fasa ƙauri a Najeriya ne su ka fitar da siriin a ƙarshen makon da ya gabata.

A na zargin yan bindigan na shirin kai hare-hare kan sansanin sojoji da ke iyakokin ƙasar.

Tuni aka ɗauki matakin tsaurara matakan tsaro da kuma ƙara yawan jami’an don ganin an daƙile hakan tare da ci gaba da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Najeriya na fuskantar barazanar tsaro a wasu daga jihohin Kudanci da arewacin ƙasar wanda hakan ke silar rasa rayukan mutane masu yawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: