Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kamfanin sada zumunta na Tuwita ya amince wa dukkanin sharudan da ta shimfiɗa kafin bayar da damar ci gaba da aiki a ƙasar.

Minsitan ƙwadago a ƙasar Festus Keyamo ne ya sanar da haka bayan kwamitin da aka kafa don tattaunawa da ɓangaren gwamnatin sun bayar da rahoton su.

Ya ce gwamnatin ƙasar ta ɗage takunkumin da ta sakawa kamfanin tare da gindaya wasu sharuɗa kafin kamfanin ya ci gaba da aiki a Najeriya.

Daga cikin sharuɗan da aka saka akwai buɗe ofishin kamfanin a ƙasar, bayar da haraji da kuma kiyaye dukkanin abin da su ka shafi tsaron ƙasar.

Waɗannan na daga cikin sharuɗan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya zayyana yayin da yake jawabi a ranar tunawa da samun ƴancin kai a Najeriya.

An dakatar da amfani da shafin a Najeriya bayan da kamfanin ya goge wani rubutu da shugaban Najeriya ya yi da kuma zargin taimaka wa wani bangare da gwamnatin ta ce hakan barazana ce ga tsaron ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: