Daga Amina Tahir Risqua

Fiye da fasinjoji 20 da suka hada da daliban makarantar Madinatu Islamiyya da ke karamar hukumar Bagwai a jihar Kano, ake fargabar sun mutu a cikin wani jirgin ruwa a Kano.

Jirgin ruwan ya kife ne a kan hanyarsa daga kauyen Badau zuwa garin Bagwai.

Daliban da suka rasu, an ce suna kan hanyarsu ta zuwa ne domin halartar Mauludi domin tunawa da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad.

A cewar wata majiya a babban asibitin Bagwai, fasinjoji sama da 40 ne suka hada da daliban makarantar Islamiyya.

 

Majiyar ta kara da cewa kawo yanzu an gano gawarwaki kusan 20 kuma an ajiye su a dakin ajiye gawa na asibitin.

 

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Malam Saminu Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa hukumar kashe gobara na ci gaba da aikin ceto da misalin karfe 9:15 na dare.

 

A cewarsa ya zuwa yanzu, an gano gawarwakin daliban da abin ya shafa da na sauran fasinjoji 20.

 

Ya kuma bayyana cewa jirgin na dauke da fasinjoji sama da 40 kuma an ceto 7 daga cikinsu.

Ya ce “Yayin da mu ke magana tawagar ceto suna can suna aiki kuma ya zuwa yanzu an gano gawarwaki 20 da suka mutu yayin da 7 kuma aka tsince da ran su.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: