Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Boss Mustapha ya ce gwamnatin kasar na duba hanyoyin da za a takaita yaɗuwar jama’a a fadin kasar.

Boss Mustapha ya bayyana haka ne yayin da ya je wani taron ƙaddamar da littafi a Abuja.
Ya ce adadin yawan mutanen Najeriya na firgita gwamnati kuma za a fara duba hanyoyin da su ka dace domin shawo kan yawan nasu.

Ya kara da cewa Najeriya na iya zama kasa ta uku a duniya cikin kasashen da ke da yawan jama’a.
