Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya a Kaduna ya ce za su gurfanar da malaman makarantar su 233 waɗanda aka gano su na amfani da takardun jabu a gaban kotu.

Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya sallamar malaman makaranata na bogi 233.
Shugaban hukumar ilimin bai ɗaya a jihar Tijjani Abdullahi ne ya sanar da haka a shafin sa sadarwar zamani, wanda ya ce an gano malaman bogin ne bayan tuntuɓa da gwamnatin ta yi.

Gwamnatin ta tuntuɓi makarantu domin tabbatar da malaman da hukumar ta ga sunayen su a tabbatar su na aiki a makarantun.

Daga cikin makarantun da aka bibiya akwai wadda aka sami takardiun bodi na malaman guda 212daga cikin 233 da aka gano.
Wannan wani mataki ne da gwamnatin ta ɗauka domin farfaɗo da harkar ilimi a jihar Kaduna.
Sannan hukumar ta ce za ta ci gaba da bibiya tare da tantance takardun malamai da kuma wurin da aka tura su aiki domin tabbatar da komai na tafiya kamar yadda ya ke a cikin stari.
An gano malamai 233 da ke amfani da takardun bogi kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin karɓar hukunci.