Ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen arewa maso yammaicn Najeriya sun lashi takobin taimaka wa wajen yaƙi da ƴan bindiga da su ka gagari jama’a.

Shugaban ƙungiyar Yarima Sulaiman Ibrahim ne ya bayyana haka a cikin shirin Ana Yi Da Kai da aka gabatar a Matashiya TV ranar Laraba.
Ya ce ƙungiyar na da rawar da za ta taka a kan yaƙi da yan bindiga ta hanyar shirya addu’o’u da kuma tarukan wayar da kan masu buƙata ta musamman a kan illar hakan.

Sannan kungiyar za ta samar da horon sana’o’i ga masu bukata ta musamman domin kawar da tunanin su kan zaman kashe wando.

Yarima ya ara da cewa hatta gudagu da makafi ma za su bayar da gudunmawar don yaƙi da yan bindiga.