Connect with us

Labarai

Makafi, Guragu Da Kutare Sun Lashi Takobin Yaƙi Da Ƴan Bindigan Da Su Ka Gagari Jama’a

Published

on

Ƙungiyar masu buƙata ta musamman reshen arewa maso yammaicn Najeriya sun lashi takobin taimaka wa wajen yaƙi da ƴan bindiga da su ka gagari jama’a.

Shugaban ƙungiyar Yarima Sulaiman Ibrahim ne ya bayyana haka a cikin shirin Ana Yi Da Kai da aka gabatar a Matashiya TV ranar Laraba.

Ya ce ƙungiyar na da rawar da za ta taka a kan yaƙi da yan bindiga ta hanyar shirya addu’o’u da kuma tarukan wayar da kan masu buƙata ta musamman a kan illar hakan.

Sannan kungiyar za ta samar da horon sana’o’i ga masu bukata ta musamman domin kawar da tunanin su kan zaman kashe wando.

Yarima ya ara da cewa hatta gudagu da makafi ma za su bayar da gudunmawar don yaƙi da yan bindiga.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

NDLEA Ta Lalata Haramtattun kwayoyin A Legas Da Osun

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar lalata haramtattun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta samu nasarar ne a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi da ta kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta lalata haramtattun kwayoyin ne da ta kama a bainar jama’a a Badagry da ke jihar Legas.

Shugaban hukumar ta kasa, Mohamed Buba Marwa ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin kotu ne.

Buba Marwa ya yi kira domin samun karin goyon bayan jama’a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya kara da cewa kwayoyin da suka kama nau’o’i ne daban-daban da suka hada da koken, kanabis da tramol.

Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, malamai, kungiyoyi da sauran wadanda suka shaida lalata kwayoyin.

Continue Reading

Labarai

Babbar Kotun Tarayya Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yiwa Ganduje

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasara a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

 

Babbar kotun ta jingine dakatarwar da shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, suka yi wa tsohon gwamnan na Kano.

 

Alƙalin kotun, mai shari’a Abdullahi Liman ya umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, kada su yi aiki da umurnin babbar kotun jihar na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

 

Mai shari’a Abdullahi ya kuma ya hana duk waɗanda umurnin babbar kotun jihar ya shafa bin umurnin, har sai an saurari ƙarar da Ganduje ya shigar ta neman a yi masa adalci a saurari ɓangarensa.

 

Wannan umurnin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar kotun jihar ta amince da buƙatar shugabannin APC na mazaɓar Ganduje ta dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

 

Shugabannin dai sun dakatar da Ganduje ne saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan Afrilu domin sauraren buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje wacce lauyansa Jazuli Mustapha ya gabatar a gabanta.

 

Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da Abubakar Daudu. Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan Najeriya, kwamishinan ƴan sandan Kano, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), da hukumar kare farar hula (NSCDC)

Continue Reading

Labarai

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabbin Kwamishinoni Guda Hudu

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda hudu tare da bayyana ma’aikatan da za su fara aiki.

 

Manema laba sun rawaito Gwamnan ya ambata cewa Mustapha Rabi’u kwankwaso a matsayin kwamishinan ma’aikatar matasa da wasanni, sai Abduljabbar Garko a matsayin kwamishinan kasa da na jihar kano.

 

Sannan an nada Shehu Aliyu yarmedi a matsayin kwamishinan aiyuka na musamman sai Adamu Aliyu kibiya kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar.

 

Gwamnan ya Kuma ja hankalinsu da su zama masu gaskiya da rikon Amana a dukkannin lamuransu na yau da kullum.

 

Ya kuma bukace su da su maida hankali wajen tayashi sauke nauyin da al’ummar jihar kano suka dora masa.

 

In za a iya tunawa majalisar dokokin jihar kano tun a watan da ya gabata ne ta kammala aikin tantance sunayen sabbin Kwamishinonin da gwamnan ya tura musu domin nada su a matsayin Kwamishinoni.

 

Har ila yau a wannan rana gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin masu bashi shawara da suma majalisar dokokin jihar kano ta sahalle masa ya nada su.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: