Wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne sun sace wasu mutane 15 yayin da sun ke kan hanya a jihar Borno.

An sace mutafiyan sannan aka shiga da su cikin dajin Sambisa a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Mayaƙan sun dakatar da motar matafiyan sannan su ka tilasta musu shiga cikin dajin a daidai ƙauyen Gumsuri.

Matafiyan sun nufi jihar Adamawa daga Borno kuma mayaƙan sun yi shigar sojoji sannan su ka tare hanyar matafiyan.

Guda cikin jami’an tsaron da ya shaida wa jaridar Daily Trust lamarin ya ce yanayin shigar da su ka yi sun saje ne da jami’an tsaro lamarin da ya sa matafiyan ba su ji ɗar yayin da aka tare su ba.

Hakan ya faru ne bayan mayaƙan Boko Haram sun sace waus ma’aikatan gwamnati da ke aiki a ma’aikatar ayyuka a kan hanyar Chibok zuwa Damboa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: