Wasu ƴan bindiga sun sace mutane 42 tare da kashe wasu uku a jihar Kaduna.
ƴan bindigan sun kashe mutanen tare da sace wasu a ƙananan hukumomin Chikun da kuma Zariya.

Da farko ƴan bindigan sun shiga unguwar Gimbiya da ke ƙaramatr hukumar Chikun sanan su ka sace mutane 28 bayan sun hallaka biyu a garin.

A ranar juma’a ne dai su ka kai hari Sabon Garin Majeru da Suthen Abba da kuma Kugu duka a ƙaramar hukumar zariya sannan su ka sace mutane 14 bayan sun kashe mutum guda.

Rahotanni sun nuna cewar wanda aka kashe a Zaria mai suna Magaji Muhammad wanda kaa fi sani da Shakazulu tsohon kansila ne.

Mutanen yankin gidan Jatau sun tabbatar da kai harin wanda su ka ce abin ya ta’azzara a yankunan su.

Wasu daga cikin mazunan yankunan na yin ƙaura zuwa wasu wuraren da ba a cika kai hare-hare ba.

Kakakin ƴan sandan jihar ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar hakan wanda ya ce akwai wasu mutane biyu da su ka samu rauni kuma aka kai su babban asibitin Sabon Tasha.

Sannan an aike da isassun jami’an ƴan sanda yankunan da abin ya faru domin tabbatar da tsare rayuka da lafiya da ma dukiyoyin al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: